in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bam ya hallaka mutane 10 a tsakiyar Pakistan
2015-09-14 10:44:20 cri

A kalla mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu 43 suka samu raunuka a wani harin bam a tashar mota a yankin Multan dake gabashin kasar Pakistan.

Wani jami'in hukumar 'yan sanda a yankin Azhar Akram, ya ce, harin ya faru ne a daren Lahadin nan, kuma an kai harin ne a Vehari dake yanki Multan mai cinkoson jama'a a lardin Punjab.

Akram ya ce, hukumar 'yan sandan yankin ta ce, ta gano gawar wani mutum guda da ake zargin kai harin, kuma tuni an tafi da gawar tasa asibiti domin gwajin kwayoyin halitta don tantancewa.

Sa'an nan ya kara da cewa,r an garzaya da wadanda suka samu raunuka asibitin Nishtar dake yankin na Multan, sai dai mutane 11 daga cikin su suna cikin mummunan yanayi.

Sai dai an samu bayanai masu cin karo da juna dangane da faruwar lamarin, yayin da kwamishinan 'yan sanda Zahid Saleem Gondal, ke bayyana cewar, wani mai babur ne ya dauke ababan fashewar ya yi karo da wani keke, bam din ya fashe, yayin da wani jami'in 'yan sanda ya ce, an saka bam din ne cikin wata jaka, kuma aka yi amfani da na'ura aka tada shi, amma jami'an na ci gaba da bincike.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar nauyin harin.

Firaministan kasar Nawaz Sharif, ya yi Allah wadai da kai harin, sa'an nan ya ba da umarni a ba da kykkyawar kulawa ga wadanda suka jikkata a harin.

Kazalika a madadin ministan lardin Punjab Shahbaz Sharif, kwamishinan 'yan sandan yankin Multan ya sanar da biyan diyya na rupees miliyan dubu dari 5, kwatankwacin dala dubu 5 ga iyalan kowane mamaci.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China