in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya nanata bukatar bude kofa da hakuri da juna
2017-07-08 13:10:43 cri

Shugaba Xi Jinping ya ba da wasu shawarwari yayin jawabinsa, wadanda suka hada da: tsayawa kan yanayin tattalin arzikin duniya na bude kofa, da kokarin amfanawa bangarori daban daban. A cewar shugaban, ya kamata a goyi bayan tsarin cinikayya da ya kunshi bangarori da yawa, da bin ka'idojin da aka kulla, tare da tinkarar kalubalen da ake fuskanta ta hanyar tattaunawa.

Na biyu shi ne, kokarin neman sabbin hanyoyin da za a iya bi don ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.Ya ce don cimma wannan buri, ana bukatar a kara yin hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, da kokarin samar da sabbin fasahohi, da masana'antu, da kayayyaki na zamani.

Sa'an nan shawara ta 3 ita ce, ya kamata bangarori daban daban su hada hannu don tabbatar da karin mutane sun amfana daga karuwar tattalin arzikin duniya, sa'an nan a hada manufofin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma, ta yadda za a samu damar daidaita matsalolin da ake fuskanta a fannonin kyautata fasahohin masana'antu.

Ban da wannan kuma, shawara ta 4 da shugaban kasar Sin ya gabatar ita ce, a yi kokarin daidaita tsarin tattalin arzikin duniya, da kara musayar ra'ayi, yayin da ake tsara manyan manufofin tattalin arziki, da shiryawa tunkarar haddura a kasuwannin hada-hadar kudi, tare da kokarin ganin ayyukan da suka shafi hada-hadar kudi sun taka rawa ta fuskar taimakawa masana'antu.(Bello Wang)


1  2  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China