Sama da rumfunan zabe 66,000 ne aka bude don jefa kuri'u a fadin kasar ta Faransa, kuma an bude rumfunan zaben ne tun da misalin karfe 8 na safe agogon kasar wato karfe 6 agogon GMT, kuma an tsara gudanar da zaben har zuwa karfe 8 na dare wato karfe 6 na yamma agogon GMT a manyan biranen kasar, amma a sauran yankunan kasar za a rufe rumfunan zaben ne da misalin karfe 7 na yamma agogon kasar wato karfe 5 na yamma agogin GMT.
A kalla mutane miliyan 47 ne ake sa ran za su kada kuri'un su a lokacin zaben na yau Lahadi.
Sai dai da ma tuni Faransawa mazauna ketare suka kada nasu kuri'un tun a jiya Asabar, amma ba za'a fadi sakamakon zaben ba sai an kammala zaben a duk fadin kasar baki daya. (Ahmad Fagam)