A yayin jawabin da ya yi ta gidan talibijin a daren ranar Lahadin, Macron ya ce, a cikin wa'adin aikinsa na shekaru biyar masu zuwa, zai yi iyakar kokarinsa wajen dinke barakar dake tsakanin al'ummar kasar.
Kafin jawabin nasa, abokiyar takararsa Marine Le Pen ta riga ta amince da shan kaye a zaben, ta kuma taya Macron murnar lashe zaben.
A nasa bangaren, shugaba Francois Hollande na kasar Farsansa, ya ba da sanarwa a daren wannan rana, inda ya ce ya riga ya taya Macron murnar lashe zaben.
Za a kawo karshen wa'adin aikin Hollande a ranar 14 ga wata. Bisa yadda aka saba, shugaba mai ci da shugaba mai barin gado za su tabbatar da lokacin bikin mika ragamar mulkin kasar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, da shugaban kwamitin kungiyar EU Jean - Claude Juncker da dai sauransu sun taya Macron murnar lashe zaben shugaban kasa. (Bilkisu)