in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da rawar da shawarar ziri daya da hanya daya za ta taka wajen dunkulewar Afirka
2017-07-04 10:55:27 cri

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina mohammed ta yaba da rawar da shawarar ziri daya da hanya daya za ta taka a kokarin da nahiyar Afirka ke yi na dunkulewa waje guda.

Amina ta bayyana hakan lokacin da take jawabin yayin bikin bude taron kolin kungiyar AU da ya gudana jiya a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Ta ce, da farko an yi kira ne ga abokan hulda na kasa da kasa da su kara zuba jari a bangaren muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a a nahiyar, a wani mataki na dunkulewar tattalin arzikin shiyyar.

Jami'ar ta MDD ta ce yanzu haka kungiyar AU na kokarin kawo karshen tashe-tashen hakulan dake addaban wasu sassan nahiyar, da kafa yankunan cinikayya cikin 'yanci, don haka ta yi kira ga nahiyar da ta ci gajiyar shawarar ziri daya da hanya daya don inganta makomar nahiyar.

A shekarar 2013 ne dai kasar Sin ta gabatar da wannan shawara da nufin hade yankunan Asiya da Turai da kuma Afirka, har ma da tsohuwar hanyar cinikin siliki da kayayyakin more rayuwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China