in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin kungiyar AU
2017-07-04 09:59:53 cri

A jiya Litinin ne aka bude taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na 29 a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, bisa taken "cin gajiyar banbance-banbancen kasashen nahiyar ta hanyar zuba jari a bangaren matasa".

A jawabinsa na bude taron, sabon shugaban hukumar zartarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat, ya yabawa shugaba Paul Kagame na Rwanda da tawagarsa dangane da gudummawar da suka bayar wajen aiwatar da wasu gyare-gyare da suka kai ga nasarar gudanar da wasu muhimman ayyukan a cikin kungiyar.

Shugaba Faki ya nanata cewa, muhimman batutuwan da kungiyar za ta mayar da hankali a kan su su ne yanayin da ake ciki a kasashen Sudan ta kudu, da Somaliya, Libya da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya. Sauran sun hada da zaman tankiyan dake tsakanin Djibouti da Eritrea, da matsalar da ake fuskanta wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali, da turka-turkar siyasar da ake ciki a Jamhuriyar Demokiradiyar Congo da Guinea da sauransu.

Ya kuma yi kira ga jam'iyyun gama kai da sassa masu zaman kansu da ragowar masu ruwa da tsaki, da su hada kai a kokarin da ake na samar da agajin kai a wasu sassan nahiyar sakamakon matsalolin fari da ayyukan ta'addanci.

A nata jawabin, mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed, ta ce taken taron kungiyar na wannan karo wanda ya mai da hankali kan matasa, wata babbar matashiya ce ga manufofin ajandar samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 gami da ajandar raya nahiyar ta Afirka nan da shekarar 2063.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China