in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afirka na kokarin samar da kudaden tafiyar da harkokin AU
2017-07-04 10:28:33 cri

An yi kira ga shugabannin kasashen nahiyar Afirka dake halartar taron kolin kungiyar AU karo 29 a birnin Addis Ababan kasar Habasha, da su dauki matakan da suka dace na samarwa kungiyar kudaden tafiyar da harkokinta.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe shi ne ya yi wannan kira lokacin da ya ke jawabi a bikin taron kolin kungiyar. Yana mai cewa, ta haka ne kadai kasashen mambobin kungiyar za su yi alfahari da kungiyar, har ma ta amsa sunanta.

Kungiyar AU dai ta sha nuna damuwa game da matsalar kudaden tafiyar da harkokinta, matakin da ya haifarwa kungiyar nakasu a kokarin da ta ke na aiwatar da jerin manufofin da ta tsara, biyo bayan wagegen gibin kasafin kudin da ta ke fuskanta.

A yayin taron kolin kungiyar da ya gudana a shekarar da ta gabata a birnin Kigalin kasar Rwanda ne dai kungiyar ta bukaci kasashe mambobinta da su ba da kaso 0.2 cikin 100 na kudin kayayyakin da ake shigarwa cikin kasashen nasu a matsayin hanyoyin tara kudaden tafiyar da harkokin kungiyar, don rage dogaro kan kudaden da kungiyar ke samu daga abokan hulda.

Bayanai na nuna cewa, kasashen Kenya, Rwanda, Chadi, Habasha, Jamhuriyar demokiradiyar Congo da Ghana na kan gaba wajen aiwatar da wannan shiri na tattara kudaden tafiyar da harkokin kungiyar.

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed ta yabawa matakin shugabannin nahiyar na nemawa kansu madogara, kamar yadda suka yanke shawarar daukar nauyin kaso 25 cikin 100 na asusun wanzar da zaman lafiya da tsaro na AU nan da shekarar 2020.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China