Kungiyar tarrayyar kasashen Afrika AU ta jaddada mahimmanci dake akwai na kara inganta huldar aiki tare da MDD domin zaburar da zaman lafiya da tsaro.
Shugabar kungiyar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini Zuma ita ce ta yi wannan kiran a yayin da ta ziyarci Addis Ababa, babban birnin Ethiopia domin halartar wata tattaunawa tsakanin kungiyar ta AU da wata tawagar MDD da kuma wasu masu fada a ji daga Afrika.
A yayin da suke musayar ra'ayi, Nkosazana ta ce, ana yin amfani da sharuddan kwamitin tsaro na MDD a dukanin ayyukan samar da zaman lafiya na Afrika domin samar da zaman lafiya a duniya.
Ta jaddada mahimmancin dake akwai na kara dankon hulda tsakanin AU da MDD domin taimakawa wajen tunkarar matsaloli masu tasowa da kuma samar da hanyoyi na karfafa hulda tsakanin bangarorin biyu. (Suwaiba)