in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an AU da MDD na taro a Habasha don duba matsalar tsaro a Afirka
2015-03-13 09:47:40 cri

A jiya ne jami'an kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka (AU) da na kwamitin tsaron MDD suka hallara a birnin Addis Ababa na kasar Habasha don tattauna kalubalen tsaron da ke addabar nahiyar Afirka.

Taron na shekara-shekara zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a yankin Great Lakes, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali, yankin Sahel, Libya, Sudan ta Kudu, Somaliya da Darfur da kuma batutuwan da suka shafi matakan yaki da kungiyar Boko Haram.

A jawabinsa yayin taron wakilin musamman na babban sakataren MDD Haile Menkerios ya ce, duk da irin nagartattun matakai da ake dauka, har yanzu bai ji dadin rashin samun wani ci gaba a shirin samar da zaman lafiya na Sudan ta Kudu ba.

Ya ce, cikin 'yan makonni masu zuwa MDD za ta karfafa kokarin shiga tsakani da kungiyar IGAD ke yi a gabashin Afirka.

Sai dai ya ce, ya gamsu da irin ci gaban da kasashen da ke yankin tafkin Chadi da Benin suka cimma tare da taimakon kungiyar AU da MDD wajen kafa rundunar hadin gwiwa a kokarin da ake na yakar mayakan Boko Haram.

Wakilin na MDD ya bayyana cewa, rashin shugabanci na gari shi ke haifar da matsalar rashin tsaron da nahiyar ke fuskanta a halin yanzu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China