Shugaban ofishin kula da cudanya da kasashen waje a hukumar wasanni ta kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin Song Luzeng, ya bayyana a gun bikin rufe gasar cewa, wasanni muhimmin kashi ne a fannin mu'amalar al'adu, kuma kasashen BRICS na da kwarewa a wasanni iri iri, kana suna da al'adun wasanni.
Ya ce yayi imani da cewa, gudanar da gasar wasannin kasashen BRICS cikin nasara, za ta sanya kaimi ga hadin gwiwar wasannin, da bunkasa mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen BRICS. Ta hanyar wasanni za a hada matasan kasashen BRICS da juna, don kirkiro kyakkyawar makoma tare.
'Yan wasa daga kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Afirka ta Kudu da Sin kimanin 300 ne suka halarci gasar a wannan karo. Kasar Sin ta tura tawaga mai mutane 53, ciki har da 'yan wasa 32 don halartar dukkan wasannin da aka gudanar. (Zainab)