in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Galibin al'ummar kasar Sin sun fi aminta da hawa kekuna da motocin haya
2017-06-28 09:43:03 cri
Hukumar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta ce galibin al'ummar kasar Sin sun fi aminta da hawa keke ko shiga motar haya.

Ma'aikatar sufuri ta kasar ta fitar da wasu ka'idojin amfani da kekuna da motar haya a jiya Talata, inda ta nemi mutane su yi tsokaci a kai.

Akwai sama da kamfanoni masu motocin haya 40 a kasar Sin, kuma kamfanonin sun mallaki motoci sama da 40,000 da ke amfani da tsaftataccen makamashi.

A cewar cibiyar binciken cinikayya ta intanet na kasar Sin, ya zuwa karshen bara, akwai mutane miliyan 18.9 dake amfani da kekunan haya a fadin kasar, inda ake sa ran adadin zai kai miliyan 50 zuwa karshen shekarar nan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China