in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gabatar da shirin ta na shekaru biyar na fadada hanyoyin sufuri
2017-03-01 10:18:49 cri
A jiya Talata ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar da shirinta na fadada hanyoyin sufuri a lokacin da take aiwatar da shirinta na raya kasa na 13 daga shekarar 2016-2020.

Ministan Sufuri na kasar Sin Li Xiaopeng shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa kasar ta Sin tana fatan nan da shekarar 2020 tsawon layin dogo zai kai ga kilomita 150,000 a kasar, a yayin da hanyoyin mota za su kai kilomita miliyan biyar kuma filayen jiragen za su kai sama guda 260, baya ga tashoshin jiragen ruwa 2,527 wadanda jiragen ruwa masu nauyin tan 10,000 za su rika amfani da shi.

Bugu da kari,nan da shekara ta 2020 din, kasar Sin tana shirin kara fadada hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya wadanda za su kai nisan kilomita 30,000, inda ake fatan za su hade sama da kashi 80 cikin 100 na biranen kasar dake da yawan al'umma sama da miliyan 1.

Ministan ya kara da cewa, kasar Sin za ta kebe zunzurutun kudi har Yuan triliyan 15, kwatankwacin dala triliyan 2.17 a bangaren ayyukan sufuri a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, Wannan adadi ya hada da Yuan triliyan 3.5 da aka tanadarwa hanyoyin jiragen kasa, sai yuan triliyan 7.8 wanda za a kashe wajen gina hanyoyin mota, yayin da aka warewa sufurin ruwa Yuan biliyan 500.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China