in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jinjinwa kungiyar kasashen yammacin Afrika bisa nasarorin da ta samu a fannoni daban-daban
2017-05-30 12:12:06 cri
Tarayyar Afrika AU ta yabawa nasarorin da kungiyar raya kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ta samu a fannoni daban-daban da suka hada da inganta hadin kan yankin.

A jiya Litinin ne Kungiyar ECOWAS ta gudanar da wani biki da ya jibanci cika shekaru 42 a harabar hedkwatar AU a Addis Ababa babban birnin Habasha, mai taken 'ECOWAS a shekaru 42: waiwaye da buri".

A jawabinta, Amira Al-Fadil kwamishinar kula da walwalar al'umma ta AU, ta jadadda cewa, ECOWAS ta cimma nasarori a fannoni daban-daban.

Amira Al-Fadil, ta ambato hadin kan yankin da tabbatar da tsarin demokaradiyya da siyasa da wanzar da zaman lafiya a matsayin wasu daga cikin muhimman bangarori da kungiyar ta samu nasara cikinsu.

Kwamishinar ta AU, ta kuma bayyana ECOWAS a matsayin abar koyi ga sauran kungiyoyin yankuna a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China