in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afirka sun kaddamar da cibiyar binciken cututtuka
2017-03-09 09:29:26 cri

Hukumomin lafiya na kasashen yammacin Afirka, sun kafa cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta shiyya ko CDC a takaice, a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Da yake karin haske game da hakan, babban daraktan hukumar lafiya ta yammacin Afirka Dr. Xavier Crespin, ya ce cibiyar za ta taimaka matuka wajen gudanar da bincike kan cututtuka masu saurin kisa kamar Ebola da dai sauran su.

Kaza lika Dr. Crespin, ya bayyana wa mahalarta taron masu ruwa da tsaki, cewa cibiyar CDC za ta share fagen shirin tunkarar matsalolin lafiya kan lokaci, da sanya ido kan cututtuka a nahiyar, da horas da jami'an lafiya, da bunkasa bincike kan cututtuka iri iri.

Dr. Crespin dai na jawabi ne ga mahalarta taron kaddamar da cibiyar da ya gudana a birnin Accra na kasar Ghana. Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya, da kuma shugaban Ghana Nana Akufo-Addo.

Ya ce, Ghana ce za ta kasance sansanin horas da jami'an da za su yi aiki a sabuwar cibiyar ta CDC, inda za a yi amfani da shirin kasar na binciken cututtuka da ba da horo ko FELTP a takaice karkashin jami'ar Ghana domin inganta aikin cibiyar.

Har wa yau cibiyar ba da horo kan ayyukan wanzar da zaman lafiya ta Kofi Annan, ita ma za ta zamo jigo wajen samar da ma'aikata da za su yi aiki a wannan cibiya.

A baya dai cutar Ebola ta hallaka mutane da yawan su ya kai 11,300, ta kuma shafi mutane 28,500, kamar dai yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China