Bisa jimilla mutane 93 ne suka bace sakamakon lamarin. Kawo yanzu an riga an kammala aikin ceto a mataki na farko. Daga bisani kuma za a dora muhimmanci kan tsugunar da wadanda bala'in ya shafa, da yaki da yaduwar cuta, da kawar da yiwuwar sake abkuwar hadarin da dai sauransu. (Fatima)