Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya shugabanci taro mai taken "yanayin ci gaba yayin da ake yin kwaskwarima kan sha'anin kimiyya da fasaha a sabon zagaye", inda ya jaddada cewa, kwaskwarimar da ake yi a wannan zagaye, ba iri daya ce da wadda ta gabata ba, kuma ya kamata a rike wannan dama tare da kirkiro sabon tsari ta hanyar zurfafa kwaskwarima, da fadada bude kofa.
Li Keqiang ya ce idan aka kwatanta kwaskwarimar wannan zagaye da ta lokacin da ya gabata, yanzu akwai sabbin ayyukan da ake gudanarwa wadanda ba a gudanar a lokacin da ya gabata ba. A fannin tattalin arziki kuma, an samu sabbin bukatu, yayin da ake yin kwaskwarimar, wanda ya canja tsarin bukatu, tare da canja tsarin bunkasuwar tattalin arziki. Ya ce tilas ne a gano irin wannan yanayi, a shirya tinkarar canjin da watakila za a samu a nan gaba. (Zainab)