Littafin mai taken "Xi Jinping: dabarun kula da kasar Sin", ya kushi babi 79 na wasu jawabai da bayanan da shugaba Xi Jinping ya gabatar, tsakanin shekarar 2012 da ta 2014. Ana ganin wannan littafi a matsayin hanyar fahimtar dabarun shugabanci na kasar Sin, da kuma fasahohin kasar a fannin neman ci gaban kasa.
Bayanai masu muhimmanci da littafin ya kunsa sun janyo hankulan manyan kusoshin kasashe daban daban. Cikinsu firaministan kasar Cambodia Hun Sen ya nemi samun wani kofin littafi na musamman wanda zai iya karanta shi kan wayar salularsa, yayin da firaministan kasar Thailand, Prayut Chan-o-cha, ya gabatar da littafin ga ministocin kasarsa. A nashi bangaren, shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya sayi littafin domin abokan aikinsa da shi kansa. A cewarsa, ta hanyar karanta littafin, zai sa a samu damar fahimtar mene ne ' tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin'.(Bello Wang)