in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Red Cross: Mafi yawan mutuwar da masu dauke da makamai ke haddasawa a birane ne
2017-06-21 10:08:50 cri

Yayin da duniya ke gudanar da bikin ranar 'yan gudun hijira ta duniya a ranar Talata, hukumar bayar da agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa, mafi yawan rahotannin hare hare na baya bayan nan da masu dauke da makamai ke kaddamarwa a cikin birane ne.

Rahoton mai taken "Na ga birnina ya mutu" ya nuna cewa, yake yake na karni na 21 suna faruwa ne a cikin birane, yake yake a cikin biranen ya zama tamkar al'ada, kuma yake yaken suna faruwa ne a gidajen mutane, a kofar gidaje, kan tituna, makarantu da asibitoci.

Rahoton ya kara da cewa, a yake yaken cikin biranen, yawanci fararen hula ne aka fi hallakawa.

Rahoton yana nuna cewa, a shekaru uku da suka gabata, kashi 70 cikin 100 na dukkan fararen hula da suka mutu a Iraq da Syria ya faru ne a cikin birane, yayin da tsakanin shekarun 2010 da 2015 kusan rabin fararen hular da suka mutu a yake yake a duniya baki daya ya faru ne a kasashen Syria, Iraq, da Yemen.

Rahoton ya ce, yake yake a biranen ba yana rusa gidajen mutane ba ne kadai, har ma yana wargaza yanayin zamantakewar iyalai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China