Shugabannin rundunar sojojin kasashen Aljeriya, Mali, Mauritaniya da Nijar za su yi wani zaman taro daga bakin ranar Talata har tsawon kwanaki uku a birnin Tamanrasset dake kuriyar kudancin kasar Aljeriya domin kimanta matsalar tsaro da ake fuskanta a shiyyar yankin Sahel, in ji ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
A cewar wannan majiya, a cikin shirin kimanta matsalar tsaro da ake fuskanta a shiyyar yankin Sahel, kuma bisa aiwatar da kudurorin da aka cimma wajen yaki da ta'addanci da manyan laifuffukan kasa da kasa a cikin kwamitin shugabannin sojojin dake aiki cikin hadin gwiwa, za'a bude wani taron kwamitin shugabannin rundunar sojojin kasashen Aljeriya, Mali, Mauritaniya da Nijar daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Janairun shekarar 2015 a Tamanrasset.
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta jaddada cewa, manyan jami'an sojojin kasashen hudu za su gudanar da aikin musanyar bayanai da bincike da kuma tsara sakamakon ayyukan, kamar yadda matakan yaki da ta'addanci da manyan lafuffukan kasa da kasa da kasashen hudu suka cimma suka tanada.
Ganin suna kewaye da wani yankin da kungiyoyin ta'addanci, da ma wasu kungiyoyin dake aikata manyan laifuffukan kasa da kasa suke yawan amfani da shi, musammun ma a arewacin kasar Mali da kuma Libiya, kasar Aljeriya na fatan kafa wata hulda tare da wadannan kasashen dake makwabtaka da ita domin yaki da wadannan annoba. (Maman Ada)