Wakilin din-din-din na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka jakada Zhong Jianhua ya bayyana cewa, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen mai do zaman lafiya da kwanciyar hankali a wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula a Afirka.
Zhong wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani taron karawa juna sani game da hadin gwiwar Sin da Afirka kan zaman lafiya da tsaro da aka gudanar a Nairobi na kasar Kenya ya ce, Sin za ta bayar da gudummawar kudi da kayan aiki don karfafa yanayin tsaro a Afirka.
Ya ce, bullar sabbin ayyukan ta'addanci da wasu nau'o'in manyan laifuffuka za su kawo illa ga muradun Afirka da Sin baki daya, sai dai ya ce, duk da 'yan matsalolin da ake fuskanta a nahiyar Afirka, makoma ce mai haske a fannin harkokin tattalin arziki da zuba jari.
Jakada Zhong ya ce, kasar Sin za ta hada kai da kungiyoyin AU don daidaita rikicin da ke faruwa a Sudan ta Kudu, jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali da kuma Somaliya.
Masana daga nahiyar Afirka da ke halartar taron, sun bukaci gwamnatocin Afirka da su hada kai da kasar Sin, ta yadda za a samar da zaman lafiya a nahiyar.
Shi ma darektan cibiyar kula da harkokin tattalin arziki da ke shiyyar (IREN) James Shikwati ya shaidawa taron cewa, akwai bukatar a sake nazarin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, don magance kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar na rikice-rikice, ayyukan ta'addanci wadanda ke shafar muradun Afirka da Sin.
Taron na yini guda ya samu halartar masana da jami'ai sama da 30 daga kasar Sin, kasashen Afirka da kuma wakilai daga MDD da kungiyar AU, inda suka yi musayar ra'ayoyi game da hadin gwiwar Sin da Afirka kan samar da zaman lafiya da tsaro. (Ibrahim)