Kamfanin CRBC na kasar Sin shi ne ya dauki nauyin karatun dukkan daliban zuwa nan kasar Sin da suka halarci gasar, wadanda suke karatu a jami'o'in koyon ilmin sufuri na Beijing, da na Chang'an, da na kimiyya da fasaha na Changsha. Karkashin shirin hadin gwiwar horar da kwararru a tsakanin Sin da Afirka, ya zuwa yanzu, kamfanin CRBC ya samar da kudi ga dalibai 291 daga kasashe 6 na Afirka wato Kenya, Congo Brazzaville, Senegal, Equatorial Guinea, Angola da Togo da su zo kasar Sin su yi karatu. (Zainab)