in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Macron, da Le Pen sun kai zagaye na biyu na babban zaben kasar Faransa
2017-04-24 09:59:15 cri

Dan takara mai matsakaicin ra'ayi, kuma tsohon ministan harkokin tattalin arzikin Faransa Emmanuel Macron, da 'yar takara mai ra'ayin sassauci Marine Le Pen, sun kai ga zagaye na biyu, a babban zaben kasar Faransa da aka kada ranar Lahadi.

Alkaluman hasashe da aka fitar sun nuna cewa, Macron na gaba da kusan kaso 24 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada, yayin da Le Pen ke biya da kaso 21.8 bisa dari.

Bisa jimilla, 'yan takara 11 ne suka shiga zaben a zagayen farko, yayin da kuma a yanzu 'yan takara 2 dake kan gaba za su sake fafatawa a ranar 7 ga watan Mayun dake tafe, domin fidda wanda zai lashe zaben da rinjayen kuri'u.

Yayin wani taro bayan kada kuri'un, Le Pen ta bayyana zaben da cewa ya shiga kundin muhimman lamurra a tarihin kasar, tana mai godiya ga juriyar da magoya bayanta suka nuna.

A nasa bangare Macron, ya jinjinawa magoya bayansa, yana mai cewa cikin shekara daya, sun yi hadin gwiwar sauya alkiblar siyasar kasar Faransa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China