A yau Jumma'a ne, ofishin watsa labaru na majalsiar gudanarwar kasar Sin ya kira wani taron manema labaru, inda aka sanar da cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ta kulla yarjeniyoyi na hadin gwiwa ta fuskar masana'antu tare da kasashe fiye da 30. Ta wannan hanya kasar Sin tana taimakawa wadannan kasashe wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a.
Rahotanni na nuna cewa, kasar Sin tana kokarin daidaita ma'aunin da ake amfani da shi a nan kasar Sin a fannin masana'antu da ma'auni na duniya, a wani mataki na yada fasahohin ci gaba na kasar Sin zuwa sauran kasashe da suka rungumi shawarar "ziri daya da hanya daya", don taimakawa ci gaban tattalin arzikin wadannan kasashe. Ya zuwa yanzu, kasashen da suka hada da Habasha da Kenya sun riga sun fara amfani da ma'aunin kasar Sin a fannin samar da wasu kayayyakin gine-gine.(Bello Wang)