An samu nasarori da yawa a hadin gwiwar da ake yi a fannonin masana'antu da samar da kayayyaki karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya"
Kasar Sin tana kokarin sanya kaimi ga hadin gwiwar da ake yi a fannonin masana'antu da samar da kayayyaki, a karkashin laimar shawarar "ziri daya da hanya daya", tare da kokarin hada na'urorin sadarwa na kasashe daban daban, ta yadda za a samar da damammaki na yin hadin gwiwa don amfanin juna. Ya zuwa karshen shekarar 2016, kamfanonin kasar Sin sun yi nasarar kafa yankunan hadin gwiwar ciniki 56 a kasashen dake bin shawarar "ziri daya da hanya daya".
An gabatar da bayanin hakan ne a taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira a yau Jumma'a.(Bello Wang)