in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta amince da bude sabon ofishin yaki da ta'addanci
2017-06-16 10:21:25 cri
Zauren MDD ya amince da bukatar da babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya gabatar, ta kafa sabon ofishin da zai rika lura da ayyukan yaki da ta'addanci tsakanin kasashe mambobin majalissar. Bukatar dai ta samu amincewar mambobin majalissar baki daya.

Shugaban zaman majalissar Peter Thomson, ya ce wannan kuduri shi ne na farko, cikin muhimman sauye sauye da Mr. Guterres ke fatan gabatarwa, tun bayan da ya kama aiki a ranar 1 ga watan Janairu.

Mr. Thomson ya kara da cewa, wannan shawara za ta horewa MDD damar tallafawa kasashe mambobin ta, wajen aiwayatar da matakan yaki da ta'addanci guda hudu, wadanda suka kunshi auna yanayin yaduwar akidun ta'addanci, da auna yanayin dakile su, ko yaki da su.

Sauran matakan sun hada da gina tsarin kandagarki, da yaki da ayyukan ta'addanci a kasashe daban daban, wadanda za su karfafa rawar da MDD ke takawa a wannan fanni. Sai kuma batun tabbatar da ana kare hakkokin bil adama da dokokin kasa da kasa, a matsayin ginshikin yaki da ta'addanci.

Da yake tsokaci game da wannan batu, kakakin babban magatakardar MDDr Stephane Dujarric, ya ce Mr. Guterres yayi na'am da amincewar da kudurin na sa ya samu. Ya ce ofishin da ake fatan kafawa, zai samar da daidaito tsakanin sassan masu ruwa da tsaki, tare da bada damar tsara dabarun yaki da ta'addanci mafiya dacewa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China