in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta yi kira da al'ummar Lesotho su kwantar da hankalinsu, bayan kisan da aka yi wa Uwar gidan Thabane
2017-06-16 10:11:22 cri
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta yi kira ga al'ummar Lesotho, su kwantar da hankalinsu bayan kisan da aka yi wa Lipolelo Thabane, uwar gidan zababben Firaministan kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu Nelson Kgwete, ya yi kira ga hukumomin tsaro su tsaurara bincike kan al'amarin, don tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu.

An kashe Lipolelo ne a daren ranar Laraba, kwanaki biyu kacal gabanin  rantsar da mijinta, kuma har yanzu ba a kai ga gano dalilin kisan ba.

Nelson Kgwete ya ce gwamnatin Afrika ta Kudu na mika sakon ta'aziyya ga iyalan Thabane a wannan lokaci na jimami.

Kisan na Lipolelo ya kara jefa tsaro game da rashin kwanciyar hankali a tsarin siyasar kasar.

Thabane wanda ya lashe babban zaben 3 ga watan Yuni, zai maye gurbin firaminista mai barin gado Pakalithi Mosisili, wanda ya hau mulki bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a shekarar 2014. (Fa'iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China