Mista Ramaphosa zai yi shawarwari tare da masu ruwa da tsaki a fagen siyasa domin cigaba da kokarin tattabar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Lesotho, in ji fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu.
Ziyarar ta mista Ramaphosa na cikin tsarin shirye shiryen zaman taron manyan jami'ai na kungiyar SADC da zai gudana a ranar 28 ga watan Yuni a Gaborone na kasar Botswana, domin tattauna matsalar Lesotho. Wannan taro zai samu halatar shugabannin Batswana, Afrika ta Kudu, Mozambique, Zimbabwe, Swaziland da Tanzaniya.
A yayin ziyarar tasa a kasar Lesotho, mista Ramaphosa zai gana da firaminista Phakalitha Mosisili da kuma mambobin gwamnatinsa, mambobin jam'iyyun adawa, kungiyar sarakunan gargajiya, kwamitin malaman cocin Lesotho da wakilan kungiyoyin fararen hula domin tattauna cigaban da aka samu wajen aiwatar da matakan da aka cimma domin kawo sauye sauye kan kundin tsarin mulki da tsaro. (Maman Ada)