in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon Firaministan Lesotho ya tsere zuwa Afrika ta Kudu
2015-05-22 20:44:09 cri
Rahotanni ya tabbatar da cewar tsohon firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane ya tsere zuwa kasar Afrika ta kudu saboda neman tsira da ransa., kamar yadda kafar talabijin din SABC ta tabbatar a ranar jumma'an nan.

Hankali ya tashi a Lesotho sakamakon labarin tserewar Mr Thabane bayan harin da aka yi kokarin kai mashi, in ji rahoton.

Mr Thanbane yace bukatar shi na son jami'an 'yan sanda su bashi kariya bai samun amincewar gwamnatin kasarsa ba.

Tsohon firaministan dai wanda shi ne shugaban jam'iyar adawa ta ABC sun fadi zaben 'yan majalissar dokoki da aka yi a watan Fabrairu. Ya dai tsere ne lokacin da majalissar dokokin ke mahawara a kan kasafin kudin kasar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China