in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe dandalin tattaunawa tsakanin jam'iyyu, kwararru da kungiyoyin al'umma na kasashen BRICS
2017-06-13 10:49:13 cri

Jiya Litinin ne aka rufe taron dandalin tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa, da kwararru, da kungiyoyin al'umma na kasashen BRICS a birnin Fuzhou dake kudancin kasar Sin, inda aka zartas da shawarar Fuzhou, tare kuma da cimma ra'ayin bai daya kan shawarar da dandalin tattaunawar ilmi karo na 9 na kasashen BRICS ya gabatar, game da shawarwarin shugabannin kasashen BRICS da za a shirya a Xiamen na kasar Sin.

Sashen kula da hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne ya kira wannan taro. Taron shi ne irinsa na farko da ya gudana, a tsakanin jam'iyyun siyasa, da kwararru, da ma kungiyoyin al'umma tun bayan kafuwar tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS.

Mahalartan taron suna ganin cewa, yin cudanya sosai a tsakanin bangarorin uku, wanda ya samar da yanayi mai kyau wajen shirya shawarwarin shugabannin kasashen BRICS da za a gudanar a watan Satumba a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin, kana ya nuna goyon baya ga hadin kai tsakanin kasashen a fannoni da dama. Daraktan ofishin nazari na sashen kula da hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma babban sakataren majalisar kula da hadin kan kwararru na kasashen BRICS, ta bangaren Sin Mista Luan Jianzhang ya bayyana cewa, taron dandalin ya samu nasarori a fannoni guda uku:

"Da farko, an karfafa fahimtar juna da amincewa da juna tsakanin jam'iyyun siyasa, da kwararru, da kungiyoyin al'umma na kasashen BRICS, ciki har da kasashe masu tasowa. Ba shakka wannan ya samar da wani muhalli mai kyau wajen gudanar da shawarwarin shugabannin kasashen BRICS da za a gudanar a watan Satumba a Xiamen. Na biyu, majalisar kwararru ta kasashen BRICS ta cimma ra'ayi na bai daya, kan shawarwarin da za a gabatar ga shawarwarin Xiamen. Na karshe kuma an zartas da shawarar Fouzhou, wanda baya ga nuna ra'ayin wakilan kasashen BRICS, ta kuma bayyana na wakilan kasashe masu tasowa."

An ce, jam'iyyu 37 da kungiyoyin kwararru 105, da kuma kungiyoyin al'umma 75 da suka fito daga kasashe masu tasowa 26, ciki har da kasashen BRICS sun halarci taron dandalin. A yayin taron kuma, bangarori daban daban sun sa himma wajen ba da shawarwari bisa taken "Neman hadin kai da samun ci gaba, don kafa makoma mai kyau", kana sun cimma ra'ayi na bai daya kan yadda ake gudanar da hadin kan BRICS a sabon yanayin da ake ciki. Mataimakiyar sakataren jam'iyyar ANC ta kasar Afirka ta kudu Yasmin Duatre ta bayyana cewa, akwai bukatar a saurari muryar gwamnatoci, da jam'iyyu, da kwararru, da kungiyoyin al'umma da dai sauransu, domin inganta hadin gwiwar BRICS:

"Ba zai yiwu a cimma dunkulewar duniya baki daya cikin sauri ba. A matsayin mu na kasuwani masu tasowa, da kasashe masu tasowa, yanayin da muke ciki ya sha bamban da na kasashe masu ci gaba. A gani na, taron wannan dandali ya samar da dandamalin tattaunawa a gare mu, wanda kuma ya shigar da wasu kasashen dake da ra'ayin bai daya cikin babban gida na BRICS, wannan yana da muhimmanci kwarai."

Kasashen BRICS sun samu jerin nasarori ta ci gaba da suka samu a shekaru fiye da goma da suka gabata. A halin yanzu, hadin kan kasashen BRICS na cikin wani muhimmin mataki na samun bunkasuwa, wato a yayin da ake fuskantar dama mai kyau, kuma ana fuskantar kalubale mai sarkakiya. Shugaban zartaswa na sashen nazarin harkokin kudi na Chongyang dake jami'ar Renmin ta kasar Sin Wang Wen ya bayyana cewa, yin cudanya sosai a tsakanin jam'iyyu, da kwararru, da kungiyoyin al'umma, ya samar da damar kirkire-kirkire ga tsarin BRICS, kana kuma zai zurfafa sabon karfi na inganta hadin kan kungiyar ta BRICS:

"Da farko, wannan ne hadin kai bisa manyan tsare-tsare dake da nufin kafa tsarin duniya mai adalci, da daidaito, da kuma zaman lafiya yadda ya kamata. Na biyu, an tabbatar da hakikanin batutuwa kan taron ministoci, ciki har da hadin kai a fannonin aikin gona, da samar da kaya, da cinikayya, da musayar kudi da dai sauransu. Baya ga haka, bayan shekaru 10, hadin kai da muka gudanar ya daga matsayin tsare-tsare zuwa na al'umma. Saboda haka, wannan taron dandalin ya nuna cewa, mun soma hadin kai a tsakanin al'ummun mu a cikin shekaru 10 dake tafe nan gaba." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China