in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS sun shirya taron raya tsarin kiwon lafiya na zamani
2017-05-25 13:32:38 cri

A yayin da babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da ke gudana a birnin Geneva, an kuma gudanar da taron inganta tsarin kiwon lafiya na zamani na kasashen BRICS a karkashin jagorancin kasar Sin a birnin na Geneva, kuma jami'an kiwon lafiya da suka zo daga kasashen nan biyar na BRICS, wato Sin da Rasha da Indiya da Brazil a kuma Afirka ta kudu suka halarci taron, inda suka yi musayar fasahohi da kwarewarsu ta fannin inganta tsarin kiwon lafiya.

Kasashen BRICS su kan shirya taron kiwon lafiya a yayin babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta yadda za su rika tattaunawa da juna a kai a kai, kuma su kan jagoranci taron bi da bi. A wannan shekara, kasar Sin ce ke jagorantar taron, kuma a gun taron da aka kira a jiya Laraba, an tattauna kan yadda za a samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

Babbar darektar hukumar WHO mai barin gado Margret Chan ta halarci taron, inda a jawabinta ta yabawa kasashen na BRICS sabo da kokarin da suka yi a fannin ayyukan kiwon lafiya, baya ga haka, ta kuma jaddada muhimmancin inganta tsarin kiwon lafiya na gama gari

Liang Wannian, shugaban sashen kula da gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya na hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin shi ma ya gabatar da jawabi a gun taron, inda ya jaddada ma'anar taken taron. Ya ce, "Taken taron na da matukar muhimmanci ta fuskokin raya tsarin kiwon lafiya na gama gari da cimma burin samun dauwamammen ci gaba, haka kuma makoma ce ta ci gaban harkokin kiwon lafiya."

Daga baya kuma, malamin ya bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin raya tsarin kiwon lafiya na gama gari. Ya ce, gwamnatin kasar Sin na ba da muhimmanci a kan raya ingantaccen tsarin kiwon lafiya, kuma ta gudanar da ayyuka ta wasu fannoni hudu. Na farko, kyautata kwarewar ma'aikatan lafiya a matakin farko, ciki har da kara ware makuden kudade ga hukumomin kiwon lafiya a matakin farko, da kyautata yanayinsu da horar da kwararru. Na biyu, an gyara tsarin kiwon lafiya, inda aka bunkasa tsarin likitocin gida. Na uku, an kyautata tsarin rarraba ayyuka, inda aka karfafa hadin gwiwa a tsakanin hukumomin kiwon lafiya. Na hudu, an kara inganta sauran tsare-tsare don tallafawa wannan aiki na raya ingantaccen tsarin kiwon lafiya. A kokarin da aka yi, an saukaka hanyoyin samun hidimomin kiwon lafiya ga mazauna kasar Sin.

Har ila a yayin taron, wakilan kasashen BRICS kowanensu sun yi musayar fasahohin kasashensu ta fannin raya ingantaccen tsarin kiwon lafiya. Wakilin kasar Brazil ya ce, ya zuwa yanzu Brazil ta cimma burin bullo da tsarin kiwon lafiya na gama gari, wato ta bulo da tsarin da ya hada gwamnatin tarayya da kuma kananan hukumomin jihohi da kuma na birane, don tabbatar da aiwatar da manufofi yadda ya kamata. A Rasha kuma, an tsara manufofi, don tabbatar da cewa, kowa na iya samun hidimomin kiwon lafiya masu inganci, ciki har da samun maganin da suke bukata, don tabbatar da adalci a tsarin zamantakewar al'umma. Sai kuma a Indiya, inda nan ma aka gina cibiyoyin kiwon lafiya a unguwanni daban daban, tare kuma da tsara jerin manufofi, ta yadda kowa zai iya samun hidomomin kiwon lafiya da suke bukata. Ban da haka, a kasar Afirka ta kudu, an bullo da tsarin inshorar lafiya na bai daya wanda ya gama kowane 'dan kasar da hidimar kiwon lafiya.

Ragowar mahalarta taron na ganin cewa, kasashen BRICS sun samu ci gaban a zo a gani, musamman ma yadda suke dora muhimmanci a kan raya tsarin kiwon lafiya da ke ba da muhimmanci ga jama'a, da kuma yadda suke karkata hankalinsu daga bangaren samar da hidima zuwa wadanda ke bukatar hidimomin, wato yadda su ke kara mai da hankali a kan masu fama da rashin lafiya. Makasudin daukar wadannan matakai shi ne kar a bar kowa a baya a fannin kiwon lafiya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China