in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya ta kara tsaurara matakan dakile barazanar ta'addanci
2017-05-24 09:59:51 cri
Firaiministar Birtaniya Theresa May, ta sanar a daren Talata cewa, kasar ta kara daukar tsauraran matakan dakikle duk wata barazanar harin ta'addanci a kasar.

A cewar May, za'a girke jami'an tsaro a duk fadin kasar Birtaniya karkashin umarnin jami'an 'yan sanda, kuma za'a tura su zuwa wuraren da ake gudanar da muhimman taruka, kamar wasannin kwallon kafa da sauran muhimman bukukuwa.

May ta bayyana hakan ne a lokacin da ta jagoranci wani muhimmin taron kwamitin wanzar da tsaro a karo na biyu, wanda aka fi sani da Cobra.

An dauki matakan tsaurara tsaron ne bayan rahoton da aka fitar bayan kammala tattaunawar ta Cobra, wanda manyan hafsoshin tsaron Birtaniya suka gudanar.

Sauran bayanai game da sauye sauyen da aka aiwatar a fannin tsaron za'a gabatar da su a nan gaba, in ji firaiminista May. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China