in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya tana fama da karancin kudade
2016-12-08 13:14:28 cri

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta ce, tana fuskantar matsalar rashin kudi, da kuma biyan wasu basuka da suka hada da albashin jami'an hukumar da na 'yan wasa.

NFF ta danganta matsalar karancin kudin da take fuskanta da na rashin biyan ma'aikatan albashin nasu da cewa, halin matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi ne ta haddasa.

Wasu kafafen yada labarai na kasar sun sanar a jiya Laraba cewa, 'yan wasan kwallon kafan matan tawagar Najeriya sun lallasa tawagar Kamaru a ranar Asabar da ta gabata, sun lashe gasar kofin mata na Afrika karo na 8, sun yi barazanar sauka a wurin wasa, har sai hukumomin kwallon kafan sun biya su kudaden da suke bin su.

Wasu masana na ganin cewa, wannan hali da ake ciki zai iya gurgunta sha'anin wasannin kwallon kafan kasar a nan gaba, suna ganin cewa, rashin kudaden zai iya haifar da illa ga fannin wasannin.

Hukumar ta NFF ta ce, duk da kalubalen rashin kudi da suke fuskanta, tana kokarin daukar dukkan matakan da suka dace domin ganin ta biya 'yan wasan da jami'an hukumar hakkokinsu.

Sai dai a cikin wata sanarwa da hukumar ta NFF ta fitar ta nuna cewa, kawo yanzu ba'a tabbatar da samun kudaden ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China