Da take tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai, darakta a ofishin shirin abinci na duniya Denise Brown, ta ce yawan mutane da ke kara tsunduma cikin wannan matsala na karuwa, musamman a arewa maso gabashin Najeriya, da kasar Somalia, da Sudan ta kudu, da kuma Yemen. Ta ce tasirin wannan matsala lamari ne mai tada hankali, irin wanda ba a taba ganin irin sa a baya ba.
A nasa bangare, darakta mai kula da harkokin gaggawa da ayyukan farfado da yankuna, a hukumar abinci da ayyukan gona na MDD FAO Dominique Burgeon, ya ce tashe tashen hankula, da matsalar sauyin yanayi na hallaka dabbobi, tare da rage kyawun filayen noma, a gabar da kuma kusan kaso 80 bisa dari na al'ummar wadannan yankuna ke dogaro kan wadannan albarkatu.
Mr. Burgeon ya kara da cewa, idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, ana iya fuskantar fari irin wanda aka gamu da shi a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011 a Somalia, wanda a wancan lokaci ya sabbaba rasa rayukan mutane 250,000. Ya ce hakan ya faru ne, sakamakon yadda kasashen duniya suka yi biris da lamarin.(Saminu Alhassan)