Deng Yulin masananin kimiyan rayuwa a cibiyar dake jagorantar aikin binciken, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, manufar aikin hadin gwiwar tsakanin cibiyar nazarin fasahar kere-kere da kamfanin NanoRacks na kasar Amurka ita ce, binciko yadda yanayin sararin samaniya ke shafar kwayoyin halitta na DNA.
Bugu da kari, binciken zai yi nazarin yadda ake jirkita kwayoyin halittan gado, daya daga cikin abubuwa mafiya hadari dake shafar 'yan sama jannati dake aiki a sararin samaniya, duba da yadda suke fuskantar haske ninki 10 a sararin samaniya fiye da doron kasa.
A baya dai, an aika wasu na'urorin bincike zuwa sararin samaniya ta hanyar amfani da kumbon bincken sararin samaniya na Shenzhou-8 na kasar Sin, a shekarar 2011, da kuma wanda aka harba a shekarar 2016 ta hanyar amfani da rokar Long March mai lamba 7 ta hanyar jirgin dakon kaya na sararin samaniya mai suna Tianzhou mai lamba 1 a shekarar 2017.(Ibrahim)