A shekarar 2015, an kafa wasu rumfunan kayan lambu a kauyen Paitou dake lardin Jiangxi na kasar Sin, inda aka baiwa manoma dake fama da talauci rumfunan, tare da koyar musu fasahar zamani a fannin dasa kayan lambu, lamarin da ya sanya manoman suka samu karin kudin shiga, gami da samun damar fita daga kangin talauci.(Bello Wang)