A Jiya Asabar aka gudanar da wasan neman matsayi na 3 tsakanin kungiyoyin Burkina Faso da Ghana a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2017, wadda ke gudana a kasar Gabon. A wajen wasan, Alain Traore ya buga kwallon cikin raga, ta yadda ya taimakawa kungiyarsa ta Burkina Faso ta doke kungiyar wasan Ghana da ci 1 da nema. Hakan yasa Burkina Faso ta samu matsayi na 3 a gasar cin kofin nahiyar Afirka a wannan karo.
Kungiyar ta Burkina Faso ta taka rawar a-zo-a-gani a gasar ta bana, inda ta lashe dukkan wasannin da aka buga a zagayen rukunin wasan, ta zarce zuwa zagaye na gaba bisa matsayi na farko data samu a rukuninta. Daga baya kuma, a wasan kusa da na karshe, Burkina Faso ta yi kunnen doki da Masar da ci 1 da 1 cikin wa'adin wasan na mintuna 90, sai dai a karshe Masar ta zara tata kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.(Bello Wang)