in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta bukaci a tallafawa matasa masu sha'awar wasanni don hana su kaura zuwa wasu kasashe
2016-08-17 11:07:59 cri
Mai horas da 'yan wasan kasar Kenya wanda ya taimaka wajen horas da Ruth Jebet 'yar asalin kasar Bahrain, wadda ta lashe gudun mita 3000 rukunin mata a gasar wasannin Olympics da ke gudana a Rio, ya ce kamata ya yi kasar Kenya ta taimakawa 'yan wasan masu hazaka, a wani mataki an rage kaurar da 'yan wasan ke yi zuwa wasu kasashen da suka fi biyan kudade masu tsoka。

Barnaba Korir, jagoran shirin horas da 'yan wasa matasa na kasar Kenya, ya ce Kenya bata san irin matsanancin halin da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle suke ciki ba. Lamarin da ya ke tilasta musu canza kasarsu ta asali zuwa wata.

Ya ce, ko da yake Jebet tana zaune ne a kasar Kenya a halin yanzu, babu wanda ya damu da ya taimaka mata, musamman kasancewar ta fito ne daga iyali marasa sukuni.

Korir ya kara da cewa, Kenya bata sha'awar mutane su canza kasar su ta asali, sai dai lokaci ya yi da za'a gudanar da bincike domin gano musabbabin dake haddasa wasu 'yan wasa kaura daga Kenya inda suke canza kasar su ta asali.

Korir ya ce, ya kamata gwamnati ta bada guraben karo ilmi ga matasa da ke wasanni domin su samu abin yi bayan sun kammala harkokin wasanninsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China