Yayin wani taro na duniya kan bincike a sararin samaniya, Yang Liwei ya ce ba za a dauki lokaci mai tsawo wajen amincewa da samar wa aikin kudi ba.
Da aka tambaye shi ko yana shirin zuwa duniyar watan, Yang wanda shi ne dan sama jannati na farko a kasar Sin, ya bayyana sha'awa a fuskarsa, yana mai cewa idan an ba shi dama to babu matsala.
Shi ma shugaban hukumar kimiyya da fasaha ta sararin samaniya Wu Yansheng, ya ce kasar Sin na shirin zuwa sama jannati.
Tafiyar za ta kunshi jirgi mai dauke da mutane da na'urar da ke zuwa duniyar wata da kuma na'urar Propulsion mai dauke da man da jirge ke amfani da shi.
A cewar Wu Yangsheng, za a tura jirgin mai dauke da mutane da na'urar zuwa watan su yi zagaye daban-daban. (Fa'iza Mustapha)