Kasar Sin na tattaunawa da wasu kasashe, da kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar nazarin sararin samaniya ta Turai, kan raya cibiyar sadarwa ta kasa da kasa a duniyar wata.
Babban injiniya na hukumar kula da masana'antun kimiyya da fasaha don tsaron kasar Sin Tian Yulong, shi ne ya fadi hakan yayin da yake halartar wani taro game da ayyukan sararin samaniya a birnin Xi'an a jiya Litinin 24 ga watan nan.
An kuma labarta cewa, aikin nazarin sararin samaniya mai nisa bisa ilmin kimiyya, wani sabon aiki ne da kasar Sin ke dora muhimmanci a kai.
Kasar Sin za ta harba tauraron dan Adam kirar Chang'e mai lamba biyar a karshen shekarar nan ta bana, a kokarin cimma burin sauka a duniyar wata, da binciko albarkatun dake wurin, sa'an nan a komo doron duniya cikin nasara.
A shekara mai zuwa ma, a karon farko, dan Adam zai sauka kan sashen karshe na wata. Kuma kasancewar ba a iya sadarwa tsakanin sashen da doron duniyar mu, ya sa dole ne a raya wata cibiyar sadarwa a kan wata.
A wannan karo na farko, dan Adam zai sauka kan sashen karshe na wata, za a kuma yi bincike game da iska, da yanayin wurin, har ma da albarkatun dake wurin. (Kande Gao)