in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mukaddashin Shugaban kasa: Tattalin arzikin Nijeriya ya daina dogaro kan man fetur
2017-05-30 12:59:47 cri
Mukaddashin Shugaban kasar Nijeriya Yemi Osinbajo, ya ce tattalin arzikin kasar ya daina dogaro kan farashin danyen man fetur.

A sakonsa ga al'ummar kasar kan cika shekaru biyu na gwamnatin Muhammdu Buhari a jiya, Yemin Osinbajo ya bayyana cewa, tattalin arziki shi ne babban kalubalen da kasar ke fuskanta tun daga 2015.

Sai dai, Mukaddashin shugaban kasar ya ba 'yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatin ta tsallake matakin wahala, yana mai kira da kada su gajiya, su kara zuba ido.

Ya ce aikin gwamnatin ta fuskar tattalin arziki ya mai da hankali ne kan samar da shirye-shirye masu gajeren zango da ke da nufin rage radadin da ake ciki tare kuma da wasu na matsakaici da dogon zango da ke da nufin sake fasalin tattalin arzikin.

A cewarsa, shirye-shiryen masu gajeren zango, sun hada da ba da jerin tallafi ga jihohi dan ba su damar cike gibin da ke akwai wajen biyan albashi, al'amarin da shugaba Buhari ya bayyana matukar damuwa a kai.

Yemi Osinbajo ya kuma bayyana cewa, gwamnatin ta fara shimfida wani tsari karkashin shirinta na tallafawa al'umma, lamarin da ya bayyana a matsayin wanda ba a taba yin irinsa ba a tarihin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China