in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNFCCC: Ba za a sauya fasalin yarjejeniyar Paris ba
2017-06-02 09:31:09 cri

Sakatariyar shirin aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris ko UNFCCC a takaice, ta ce ba za a sauyawa yarjejeniyar Paris fasali ba saboda bukatar wata kasa guda.

Wata sanarwa da ofishin ya fitar, ta ce yarjejeniyar Paris da kasashe 194 suka amincewa kana 147 suka rattabawa hannu, ta kafa wani muhimmin tarihi, game da yunkurin da kasashen duniya ke yi na daukar matakan da suka wajaba, wajen dakile kalubalen sauyin yanayi.

A hannu guda, ofishin na UNFCCC ya yi takaicin ganin yadda Amurka ta ayyana ficewa daga wannan yarjejeniya, yana mai cewa, jami'ai za su zanta da bangaren Amurka, don tattauna tasirin da ficewar Amurkar ka iya haifarwa.

Sanarwar ta ce, yarjejeniyar Paris na da nufin dakile mummunan tasiri ta fuskar tattalin arziki ga daukacin kasashen duniya sakamakon sauyin na yanayi. A hannu guda kuma ana fatan kafa wani ginshiki na samar da ci gaba da tsaron duniya. Bugu da kari yarjejeniyar za ta tallafi shirin raya wasu sana'o'i, da harkokin zuba jari, da raya birane da yankuna, dama kara inganta zamantakewar al'ummar duniya.

Daga karshe dai ofishin na UNFCCC, ya alkawarta ci gaba da kokari tare da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, wajen aiwatar da wannan yarjejeniya daga dukkanin fannoni a kuma matakai na kasa da kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China