in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe wani jami'in wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan
2017-06-02 09:49:19 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Sudan UNAMID, ya sanar da kisan da wasu da ba a san ko su waye ba, suka yi wa wani jami'in shirin a ranar Laraba da ta gabata.

Sanarwar da shirin ya fitar ta ce,wasu da ba a san ko su waye ba, sun kashe wani jami'in wanzar da zaman lafiya, inda suka kai masa hari yayin da yake cikin mota a Nyala babban birnin jihar South Dafur na Sudan.

Shirin ya soki harin da kakkausar murya, yana mai bayyana shi a matsayin take dokokin kasa da kasa, inda kuma ya bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu cikin kisan.

An tura dakaru 24,000 zuwa Dafur karkashin shirin UNAMID ne a shekarar 2008, domin wanzar da zaman lafiya a yankin dake fama da yakin basasa tun daga shekarar 2003.

Tun bayan fara aiki a kasar ne jami'an ke fuskantar hare-hare da dama daga wasu kungiyoyin da ba a san su ba, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar sama da jami'ai 53. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China