in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jaddada goyon bayanta ga yunkurin magance matsalolin yankin Darfur
2017-05-16 09:49:23 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fidda wata sanarwa a jiya Litinin wadda ke cewa, kwamitin tsaro na kungiyar hadin kan kasashen Afirka ko AUPSC a takaice, ya jaddada aniyar sa, ta goyon bayan gwamnatin Sudan, a kokarin ta na kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar yankin Darfur.

Hakan dai na zuwa ne bayan da wakilan kwamitin na AUPSC suka ziyarci kasar ta Sudan, ciki hadda yankin na Darfur wanda ya sha fama da yakin basasa tun daga shekara ta 2003.

Tawagar wakilan kwamitin ta yaba da yanayin da yankin na Darfur ke ciki a halin yanzu, da kuma irin hadin gwiwa dake wanzuwa tsakanin tsagin gwamnati da na kwamitin AUPSC, baya ga kayayyakin aiki da gwamnatin Sudan din ke samarwa tawagar MDD mai aiki a yankin na Darfur ko UNAMID a takaice.

Har wa yau AUPSC ya nanata cikakken goyon bayan sa ga kasar Sudan, da matakan da mahukuntan ta ke dauka, na wanzar da zaman lafiya da lumana mai dorewa a daukacin sassan kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China