in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta shirya taron gaggawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
2017-05-09 10:26:07 cri

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, sun amince su gudanar da wani taron gaggawa ranar Lahadi mai zuwa a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi kasashen biyu.

Rahoton cibiyar watsa labarai ta kasar Sudan a jiya, ya ruwaito Mahmoud Kan, shugaban ofishin dake kula da harkokin kungiyar AU a Khartoum na cewa, kasashen biyu sun amince su tattauna a ranakun 14 da 15 na watan nan karkashin shirin kwamitin sulhu na kungiyar AU (AUHIP).

Mahmoud Kan ya ce, ministan harkokin wajen Sudan, Ibrahim Ghandour ne zai jagoranci wakilan kasar da za su halarci taron, yayin da ministan yada labaran Sudan ta Kudu Michael Makuei zai jagoranci wakilan kasarsa.

Ya kuma kara da cewa, yayin taron, za a tattauna batutuwan da suke ciwa bangarorin biyu tuwo a kwarya da suka hada da yankin da aka amince da haramtawa duk wani ayyukan soji da sauran yarjejeniyoyi da bangarorin biyu suka cimma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China