in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana neman tara dala miliyan 800 don tallafawa 'yan gudun hijira a Sudan a 2017
2017-06-01 10:21:00 cri

MDD ta bukaci kasa da kasa da su ba da gudumowar dala miliyan 804 a shekarar 2017 domin tallafawa 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta kudu dake neman mafaka a kasar Sudan.

A cewar ofishin kula da al'amurran jin kai na MDD dake kasar Sudan OCHA, kungiyoyin ba da jin kai a Sudan sun kaddamar da asusun neman agaji na shekaru masu maya wato (MYHS) na 2017-2019 da kuma shirin ba da agaji na Sudan (HRP) na 2017 domin samar da taimakon jin kan ga Sudan.

OCHA ta ce, a shekarar 2017, jimillar kudaden da ake bukata domin aikin samar da jin kai na HRP ya kai dala miliyan 804, domin amfanar da mutane kimanin miliyan 4.

OCHA ta ce, hadin gwiwar gwamnatin Sudan da MYHS shi ne irinsa na farko a Sudan, wanda hakan zai samar da sabon tsarin taimako da kuma na dogon zango.

Ta kara da cewa, wannan tsari yana wakiltar shirin samar da jin kai wanda kungiyoyin ba da jin kai ke samarwa domin shawo kan matsalolin bukatu na dogon zango da nufin tsame mutane da ke cikin halin matsananciyar bukata da marasa galihu daga barazanar da suke fuskanta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China