in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta Kudu ya bayyana tsakaita bude wuta a kasar
2017-05-23 10:40:39 cri

A jiya Litinin shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya ayyana shirin tsakaita bude wuta bisa gefe daya a duk fadin kasar bayan ya kaddamar da shirin tattaunawar sulhu ta kasa, da nufin kawo karshen tashin hankalin da ya daidaita kasar ta gabashin Afrika.

Wannan sanarwa ta zo ne kasa da mako guda bayan da farko mista Kirr ya bayyna cewa, abu ne mai wuya a iya tsakaita bude wuta a duk fadin kasar sakamakon yawaitar tashe tashen hankula da kungiyoyi masu dauke da makamai suke haddasawa a kasar, duk kuwa da irin matsin lambar da kasashen duniya ke yi na neman a kawo karshen yakin basasar da ya barke a kasar inda yake gab da shiga shekara ta hudu.

Shugaban na Sudan ta Kudu ya bayyana cewa, tsakaita bude wutar zai sa a samu kyakkyawan yanayi don fara tattaunawar zaman lafiya ta kasar, kuma za ta ba da dama ga jami'an aikin jin kai su samu damar gudanar da ayyukansu.

Sudan ta Kudu ta tsunduma cikin tashin hankali ne sama da shekaru 3 da suka gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar lakume rayukan jama'a masu yawa a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China