in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang ta karbi masu yawan shakatawa fiye da miliyan 15 a farkon rabin shekarar bana
2016-09-01 13:15:54 cri

Taron kara rubanya kokarin raya sha'anin yawon shakatawa da jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ya gabatar, ya shaidawa manema labarai cewa, a farkon watanni shida na bana, wurare masu kayatarwa 86 na jihar, sun karbi masu yawon shakawata kimanin miliyan 15.6, adadin da ya karu da kashi 19.4 cikin dari.

Kaza lika yawan baki daga kasashen waje, da jihar ta karba ya kai bubu 728.3, adadin da shi ma ya karu da kashi 9.08 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara, inda yawan kudin da masu yawon shakatawa na kasashen waje suka kashe ya kai dala miliyan 216.

Rahotanni na nuna cewa, a farkon watanni shida da suka gabata na bana, jihar tana gina ababen yawon shakatawa 304, wadanda darajar su ta kai kudin Sin RMB biliyan 24.6, adadin da ya karu da kashi 27.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Ban da wannan kuma, an samu ci gaba mai inganci ta fuskar hanyoyin zirga-zirga tsakanin kasashen waje da jihar Xinjiang. Alal misali an gudanar da bikin ziyara a kasar Kazakhstan a birnin Urumqi hedkwatar jihar Xinjiang, an kuma fidda sabbin hanyoyin yawon shakatawa ta hanyar motoci 3 zuwa Kazakhstan, da Kyrgyzstan, wadanda suka kai sabon matsayi a wannan fanni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China