in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta Kudu ya nemi taimakon al'umma wajen yaki da laifuka a kasar
2017-05-31 09:50:02 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya ce hukumomin tsaro da sassan gwamnati na bukatar hadin kan al'umma wajen yaki da aikata laifuka.

Yayin ziyarar da ya kai yankin kogin Elsies dake Cape Town wanda aka fi samun muggan laifuka, Jacob Zuma ya ce akwai bukatar a hada hannu a matsayin kasa daya, wajen tabbatar da hukunta wadanda ke sanya mutane jin tsoron zama a gidaje ko fita tituna da wuraren aiki da na ibada.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar ya kai ziyara yankin cikin kasa da wata guda.

Shugaban ya kai ziyarar farko ne a ranar 18 ga wannan wata, bayan kisan da aka yi wa wata yarinya 'yar shekara 3, wadda aka samu binne cikin wani rami maras zurfi.

An kashe yarinyar ne a daidai lokacin da sabon matsalar kashe mata ya barke a kasar.

Jacob Zuma ya kuma fadawa mazauna yankin cewa, ya sake komawa ne saboda ya duba dimbin kalubalen tsaro da ake fuskanta musammam kisan yara, da kuma yadda hukumomin tsaro za su inganta ayyukansu a yankin.

Har ila yau, ya ce ziyarar wani bangare ne, na shirye-shiryen gwamnati game da makon gamgamin kare yara na kasar, wanda ke gudana duk shekara, domin wayar da kan al'umma game da hakkokin yara da kuma jan hankalin dukkan bangarorin al'umma su kula da kuma kare yara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China