in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu ta janye nufinta na fita daga kotun ICC
2017-03-09 11:10:24 cri

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta bayyana sauya matsaya, game da manufarta ta ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC.

Fadar gwamnatin Afirka ta kudun ce dai ta aike da wata wasika, mai kunshe da wannan batu, ga mai ba da shawara ga MDD a fannin shari'a dake kasar Ayesha Johaar. Sai dai uwar gida Johaar ba ta yi karin haske game da dalilan da suka sanya gwamnatin daukar wannan mataki ba.

An dai zaci cewa, minista mai kula da harkokin kasa da kasa Maite Nkoana-Mashabane, da ministan shari'ar kasa Michael Masutha, za su gabatar da fashin baki ga zauren majalisar dokokin kasar, game da daukar wannan mataki a jiya Laraba, to sai dai kuma duk ministocin biyu ba su samu halartar zaman ba.

Hakan dai ya tunzura tsagin 'yan adawar majalissar, ko da yake daga bisani an bayyana cewa, rashin lafiya ce ta hana Mr. Masutha halartar zaman. Kuma ministan sadarwa da aka tsara za ta wakilce shi wato Faith Muthambi ita ma ba ta samu halarta ba.

Hakan ne a cewar wasu rahotanni, ya sanya Muthambi aika Johaar zuwa majalissar, wadda ta tabbatar da janye wancan mataki na gwamnati, ko da yake babu wani karin bayani da ta gabatar.

Gwamnatin Afirka ta kudu dai ta janye shirin ta ficewa ne daga kotun ICC, bayan da wata babbar kotu dake zaman ta a birnin Pretoria ta yanke hukunce a ranar 22 ga watan Fabarairun da ya shude, cewa karya doka ne gwamnati ta dauki wannan mataki, ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China