in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na gab da kammala shirya dabarun yaki da wariyar launin fata
2017-03-22 12:36:53 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya ce yayin da ake tsaka da fuskantar matsalar wariya a kasar, gwamnatin na gab da kammala shirya dabarun yaki da wariyar launin fata da abubuwan da suka dagance shi.

Jacob Zuma wanda ya bayyana haka yayin wani gangami kan ranar kare hakkin dan Adam a garin King William's, ya ce dabarun za su yi wa gwamnatin da kuma al'ummar kasar karin haske game da yaki da wariyar launin fata da sauran abubuwa dake da alaka da ita.

A ranar 21 ga watan Maris din 1960 ne, 'yan sanda suka harbe wasu mutane 69, tare da raunata wasu da dama, a lokacin da suke wata zanga-zangar lumana ta neman 'yancin yin zirga-zirga a garin Sharpeville dake gundumar Gauteng, al'amarin da ya girgiza al'ummar duniya baki daya.

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ce ta ayyana ranar 21 ga watan Maris din kowace shekara, a matsayin ranar kare hakkin dan Adam, bayan kawo karshen wariyar launin fata a shekarar 1994.

Shugaban kasar ya kara da cewa, abun bakin ciki ne, yadda har yanzu wasu ke rike da akidar a zukatansu, al'amarin da ya bayyana a matsayin take hakkin dan Adam da aka fi kyama.

Shugaba Zuma na wannan furuci ne dangane da zanga-zangar kin jinin baki da ya barke a baya-bayan nan a birnin Pretoria da wasu sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China